Home » Ɗalibai na zargin Ana yin Sama da Faɗi a Batun Bada Tallafin Karatu na Gwamnatin Kano

Ɗalibai na zargin Ana yin Sama da Faɗi a Batun Bada Tallafin Karatu na Gwamnatin Kano

..Muna iya Kokarinmu Wajen Shawo Kan Matsalar da ake Fuskanta - Gwamnati

by Salisu Hamisu Ali
0 comment 1 minutes read

A yayin da Gwamnatin jihar Kano ke ci gaba da raba tallafin karatu ga daliban manyan makarantu daga suka fito daga masarautar Kano, wasu daga cikin daliban sun koka kan yadda aikin rabon tallafin ke yin tafiyar wahainiya inda suke zargin cewa masu raba tallafin kudin na zabe wajen turawa dalibai.

Tun shekaru 3 da suka gabata ne dai dalibai suka suyi katin neman tallafin karatun kuma tun tsawon wanann lokacin suke jiran samun tallafin.

Daya daga cikin jagoran daliban da ya fito daga karamar hukumar Birnin Kano ya shaidawa jaridar Prime Time News Hausa yadda suka shafe lokaci suna zuwa tantancewa daban daban.

Haka kuma yayi zargin cewa masu tura kudin na yin zaben wanda zasu turawa cikin daliban.

Dalibin mai suna Comrade Abubakar Kabuya ya kuma yi kira ga Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da yayi bincike kan lamarin.

“Mun kawo korafinmu ne kan wanda yake turawa dalibai bangaren Maza na karamar hukumar birni.

” Mun je an tantance mu tun ranar Talata da ta gabata, amma har yanzu mun ji shiru sabanin ga ‘yan uwan mu mata wanda duk muka yi tare da su wadanda mace ce tayi musu duk an tura musu kudin.

“Muna kira ga Gwamnati ta duba wannan al’amari ayi abinda ya dace”, inji shi.

Sai dai yayin da muka tuntubi mai baiwa Gwamnan jihar Kano shawara kan bada tallafin Karatu, Asil Ibrahim ya bayyana cewa an samu tsaiko ne sakamakon tsarin takaita zirga zirgar kudi na Gwamnatin Tarayya sannan yayi alkawarin warware matsalar daliban nan bada jimawa ba.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More