Home » 2023: Obasanjo Ba Zai Iya Kawo Mazabarsa Ba —Tinubu

2023: Obasanjo Ba Zai Iya Kawo Mazabarsa Ba —Tinubu

Tinubu ya ce yana tausayin Peter Obi a zaben da za a shiga a wata mai kamawa.

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 1 minutes read

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi Peter Obi, cewa kada ya rudu da goyon bayansa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ke yi.

Tinubu ya ce goyon bayan Obasanjo ba zai kai Peter Obi ko’ina ba, saboda Obasanjo ba zai iya lashe akwatin mazabarsa ba.

“Bincikenmu mun gano Obasanjo bai taba nasarar sa wani ya lashe kujerar shugaban kasar Najeriya ba.

“Ko a Jihar Ogun babu wanda zai dogara da shi don lashe kujerar gwamna ko kansila,” in ji Tinubu ta hnnun Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tibubu, Bayo Onanuga.

Ya ci gaba da cewa, “Muna tausaya wa Peter Obi domin Obasanjo ba zai iya lashe masa akwatin mazabarsa da ke Abeokuta ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.”

Tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana yadda Obasanjo ya goyi bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019 kuma ya sha kaye a hannun Shugaba Buhari.

Tinubu ya jadadda cewa da taimakonsa Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben tare da tika Atiku da kasa.

Ya ce tarihi ne zai sake maimaita kan sa a zaben da ke kara kartowa a watan Fabrairu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo ya mara wa takarar Peter Obi na jam’iyyar ‘Labour Party’ baya.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More