Daga Ibrahim Hamisu
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Kano na zaben Gwammna Jihar Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Shugaban tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Dikko Ahmad Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan a hedkwatar hukumar zaɓe ta jihar Kano,
Farfesa Dikko Ahmad wanda malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Dr. Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.