’Yan Najeriyar su biyar na cikin wasu mutum 11 da jami’an Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Saudiyya suka kama da hodar Iblis sin a birnin Jidda na kasar.
Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Saudiyya ta ce gungun wadanda ake zargin sun boye hodar Iblis din ne a wurare daban-daban domin kawar da hankalin jami’an tsaro.
Da yake bayanin, Manjo Marwan al-Hazmi, wanda shi ne kakakin shugaban hukumar, ya ce dubunsu ta cika a wani samame da jami’an hukumar suka kai kai musu.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ta ce ’yan Najeriyar da aka kama, suna da takardun ziyarar kasar ne, wasu mutum hudu kuma mazauna a kasar ne, sauran biyun kuma bakin haure ne da suka shiga kasar ta barauniyar hanya.
Saudiyya na da tsauraran dokoki a kan ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda ake yanke wa masu fasakwaurinsa hukuncin kisa.
Dillalansa da masu amfani da shi kuma akan daure su a gidan yari ko a yi musu tara mai tsanani ko kuma a kore su daga kasar.