Home » Ana daf buɗe masallaci na farko a tarihin majalisar tarayyar Nijeriya

Ana daf buɗe masallaci na farko a tarihin majalisar tarayyar Nijeriya

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 1 minutes read

A karon farko tun bayan kafa  majalisar dokokin tarayya, za a bude masallacin sallar Juma’a da kansu salawati a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, 2023.

Da yake kaddamar da kwamitin mutum 7 na kwamitin tsare-tsare a ofishinsa a yau, shugaban kwamitin gine-ginen masallacin Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci ‘yan kungiyar da su yi aiki don ganin an samu nasara ba tare da cikas ba.

Da yake mayar da martani a madadin ‘yan kwamitin, shugaban kuma dan majalisar wakilai Hon. Engr Yunusa Abubakar ya bada tabbacin jajircewar yan kungiyar tare da godewa Ubangiji da ya baiwa yan uwa wannan aiki na Allah.

Ya kuma yi kira ga ’yan uwa da su yi sadaukarwa saboda kankanin lokacin aikin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Honarabul Sanata Nasiru Sani Zagon Daura, Hon Isiyaka Ibrahim, Ustaz Sadiq Bala Illelah, Pharm Mustafa Muhammad, Dr Sule Ya’u Sule yayin da Haruna Ibrahim Shekarau zai zama sakataren kwamitin.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More