Home » Ban Gama Bayyana rayuwar da ƙasar Hausa ke ciki ba har yanzu a fim ɗin “MANYA MATA” – Abdul Amart

Ban Gama Bayyana rayuwar da ƙasar Hausa ke ciki ba har yanzu a fim ɗin “MANYA MATA” – Abdul Amart

by Hannatu Sulaiman Abba
0 comment 2 minutes read

Hannatu Suleiman Abba

Abdulrahman Muhammad wanda a ka fi sani da Abdul Amart ya ce har yanzu bai gama fayyace abubuwan da shirin nan mai dogon zango ya ƙunsa ba game da rayuwar da ake ciki a ƙasar Hausa.

Abdul Amart wanda shi ne ya shirya Shirin MANYA MATA ya kara dace wa ,babu wata ƙungiya ko hukumar da ta ɗau nauyin shirin illa so da kishin al’umma da ya saka a gaba wajen ganin al’umma sun gyaru.

“Idan muka ce muna koyar da tarbiyya sai a yi caa a kan mu. Shirin Manya Mata ya taɓo kowanne fanni na rayuwa da al’umma Hausawa ta tsinci kanta a wanna zamani” a cewar sa.

“MANYA MATA Shirin ne da ya Shiga cikin al’umma wajen yin bincike tare da kawo gyara, baya nuna rashin kunya ko Kuma ɓata tarbiyya ko fito na fito da maza, duk da mun nuna Mata masu gwagwarmaya a sahun gaba.

“Haka na da Nasaba a kan yadda sunfi maza kafa ƙungiyoyin kwato hakkin Mata da ƙananan yara hakkin su tare da taimako a ƙasar Hausa,Inji Amart

“Da dama a ƙasar Hausa a Yanzu, idan na miji ya auri mace, kai tsaye zai ga alfarma yayi Mata, bai damu da ci ko Sha din ta ba, wulakanci da cin zarafi sunfi yawa.

“Akwai matar da muka samu labari ta sai ta siyar da mutunci ta ,kafin zata samu abinci da zata ci da Ya’yan ta.

“Hakazalika, Shirin MANYA MATA ba zai tsaya ana ba, za mu nuna amfani ilimin addini ta bangare karatun almajiranci ,domin akwai iyayen da suke Kai Ya’yan su da abinci da zasu ci, idan zasu Kai su makarantar almajiranci. domin shima malamin yana da nasa iyalan.

“A dai cikin Shirin MANYA MATA ,zamu Kara haska halin da ƙasar mu ke ciki, wato yadda cin hanci da rashawa ya addabi kasar mu,rufe boda, rashin tsaro da sauransu.

“Babban buri na game da Shirin MANYA MATA shi ne, al’umma su gyaru ,duk da Ina samu Kira a duk fadin duniya aka cewa ,an Dade ba’ayi Shirin da ya nuna halin da kasar hausa ke ciki ba kamar wanna. Sanna Shirin MANYA MATA Babu Wanda ya dau sa, zuba kudi mukayi domin mu kawo sauyi a cikin rayuwa mu, Ba muyi Shirin don samu kudi ba. Kofar mu a bude take ga wayenda suke son daukar nauyi Shirin yanzu ,bada shawara da Kuma gudumawa.

Shirin MANYA MATA zai dawo a Karo na biyu a watan Yuli a wannan shekarar.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More