Home » Engr Sagir Koki: Haske ga Al’ummar Ƙaramar Hukumar Birni

Engr Sagir Koki: Haske ga Al’ummar Ƙaramar Hukumar Birni

by Salisu Hamisu Ali
0 comment 1 minutes read

 

Daga Salisu Hamisu Ali

Zan iya cewa a karon farko karamar hukumar birni zata dace da wakili wanda a tarihinta ba a taba samun kamarsa ba.

Nagarta da gogewar Injiniya Sagir Koki abu ne a zahiri da kowanne mai hankali da tunani a karamar hukumar birni ke gani.

Abinda kullum yake bani mamaki shi ne yadda zakaga mafiya yawan masu tallata Injiniya Sagir Koki Matasa ne da suka mallaki hankalinsu, wadanda kuma suke a waye ma’ana suka san kansu.

Bana mantawa na taba zuwan siyan abinci a wani gida dake kusa da unguwarmu, kwatsam sai aka fara hirar siyasa da ‘yan takarkaru na jam’iyyu.

Ana tsaka da wannan hira ne mai siyar da abincin ta dubi Samari biyu dake kan layi tace amma dai ‘yan Samari “Sagir Koki zaku zaba ko”

Cikin karfin Gwiwa kuwa matasan nan suka amsa suka ce ay “Hajiya mutumin kirki ne kwarai da gaske”, haka itama matar tace abinda yasa nace ku zabe shi ne ” Akwai makotan unguwarsa wallahi sun fadama irin yadda yake taimakon al’umma duk da cewa baya rike da wata kujera ta siyasa”.

Irin wadannan shaida ta Alkhairi nasha jinta a wurare daban daban, bugu da kari ma har ‘yan jam’iyyun Adawa suna fadar nagartarsa.

Ay kuwa babu laifi idan nace tabbas al’ummar birni sun yi dace da farin Wakili.

Wannan kadai a iya mu’ammalarsa ce da al’ummar dake kusa da shi, Insha Allah a rubutu na gaba zan fadi irin gogewarsa kasancewarsa yayi mu’ammala da mutane daga sassan Najeriya daban-daban wanda kuma wakilci al’ummar birni yana bukatar mutumin da yasan al’umma a dukkan bangarorin kasarnan.

 

Salisu Hamisu Ali Dan Jarida ne kuma dalibi a jami’ar Bayero Kano.

salisuhamisu32@gmail.com

08176630741

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More