Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University dake Niger da Nigeriya Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa Hajiya Maryam Abacha, matar marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar danta, Abdullahi Abacha.
Abdullahi Abacha Mai shekaru 36, Da na biyun Karshe ga marigayi Sani Abacha, ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barci a gidan iyalansa da ke Abuja a ranar Asabar, 4 ga Maris, 2023.
Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyya da ya sanya wa hannu kuma ya bawa manema labarai a Kano ranar Asabar, ya bayyana rasuwar Abdullahi a matsayin abin ban tsoro da firgitarwa.
Farfesa Gwarzo, wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, Kano, ya bayyana rasuwar Abdullahi Abacha a matsayin abin mamaki idan aka yi la’akari da yadda ya rasu tun yana matashi.
“A madadin iyalai na, MAAUN Conglomerate, ina so in mika ta’aziyyarmu ga mahaifiyarmu, Hajiya Maryam Abacha da daukacin iyalinmu bisa rasuwar Abdullahi,” in ji Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyyar.
Da yake jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki, Farfesa Gwarzo ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya ba Hajiya Maryam Abacha da daukacin ‘yan uwa ikon jure wannan babban rashi.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan sallar jana’izar a babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Asabar.
Allah ya jikansa da rahama Allah ya saka shi a AlJannatul Firdaus, amin.