Wata Gobara dake ci gaba da ci a halin yanzu ta shafi Shaguna da dama a Kasuwar siyar da kayan masarufi ta Singa dake Kano.
Acewar wani shaidar gani da ido gobarar ta tashi tun tsakar daren jiya kuma har safiyar yau na ci gaba da ci.
Masu kashe gobara dai na ci gaba da kokarin kashe wutar.