Gobara ta  tashi a  gidan gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdulahi Umar Ganduje da ke titin Miyangu a Nassarawa GRA Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar wa manema labarai afkuwar gobarar a ranar Alhamis, inda ta ce gobarar ta afku ne a ranar Litinin.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya bayyana cewa tuni aka shawo kan gobarar a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa gidan.
Wakilinmu ya tattaro cewa gobarar ta tashi ne a wani wuri da Ganduje ke kiwon shanu kuma ta lalace sannan da yawa daga cikin dabbobin suka mutu sakamakon gobarar, tare da kona wasu kadarori na miliyoyin naira.
Wata majiya ta tabbatar wa wakilinmu cewa kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba amma ta fara ne a lokacin da ake yin walda da karfe a gidan yayin da ake ci gaba da aikin kawata gidan saboda komawar gwamna  Abdullahi Umar Ganduje gidan.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya ki cewa komai lokacin da aka tuntube shi.