Daga Maryam Sulaiman Muhammad
Gwamnatin jihar Kano ta dage dokar hana fita da ta sanya a jihar da nufin kaucewa tabarbarewar doka da oda biyo bayan bayyana sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da dage dokar a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin.
Ya ce an dauki matakin dage dokar ne bayan an yi nazari sosai kan lamarin da kuma kwanciyar hankali da  ya kasance a jihar.
Kwamishinan ya yi kira ga bankunan kasuwanci da ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su fito su ci gaba da sana’o’insu na yau da kullum.