Fitaccen Mawakin Hausa da tauraruwarsa ke ci gaba da Haskawa, Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya ce idan har ka daka ta ‘yan siyasa wuta zaka.
Naziru wanda a kwanakin baya yayiwa Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP na shugaban kasa wakar “APC sai mun bata Wuta” ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.
“In ka daka ta yan siyasa wuta zaka!😡”
Sai dai bayan wallafa rubutun na Sarkin Waka ya jawo ce-ce-ku-ce inda mabiyansu a shafin suka dinga mayar da martani daban-daban.