Gabanin zaben gwamnoni da ta ‘yan majalisar dokokin jihar a ranar 18 ga watan Fabrairu, kungiyar daliban jihar Kano (NAKSS), ta bayyana goyon bayanta ga jam’iyyar PDP a jihar.
Kungiyar daliban ta amince da takarar Sadik Wali, mai rike da tutar jam’iyyar da abokin takararsa, Yusuf Bello Dambatta.
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP, Sadiq Wali da abokin takararsa, Yusuf Bello Dambatta bayan sun tabbatar da zasu ciyar da Kano gaba tare da ganin hasken ci gaban jihar Kano a tsarinsu.
Ma’ajin NAKSS na kasa, Comr. Adamu Sani Galadima, a wata sanarwar manema labarai da ya sanarwa PRIME TIME NEWS, ya ce kungiyar ta yanke shawarar amincewa da dan takarar PDP ne bayan wata tattaunawa mai zurfi tare da cimma matsaya a tsakanin mambobin kungiyar.
Comr. Adamu ya yi addu’ar Allah ya sa ilimi ya zama fifiko a jam’iyyar bayan zaben gwamna na ranar 18 ga Maris.
“Bayan tuntubar juna tare da yin la’akari da kudurorin ‘yan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyu daban-daban, shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NAKSS) sun kuduri aniyar amincewa da takarar dan takarar gwamnan PDP na jihar Kano, Sadiq Wali da mataimakinsa Yusuf Bello Dambatta
“Saboda haka, muna bayyana goyon bayanmu gaba daya a gare su, kuma muna kira ga daukacin daliban jihar Kano da su fito kwansu da kwarkwatansu domin kada kuri’arsu ga jam’iyyar PDP a ranar Asabar 18 ga Maris, 2023,” in ji Galadima.
Da yake mayar da martani kan amincewa da kungiyar daliban, dan takarar mataimakin gwamna, Yusuf Bello Dambatta ya sha alwashin ba da fifiko kan ilimi idan aka zabe shi.
Ya kuma zargi APC da NNPP da yin wasa mai datti a fagen siyasar jihar.