Kwamitin karbar mulki na jam’iyyar NNPP a Kano ya bayyana yadda Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta karkatar da kudin kananan hukumomi Biliyan 100.
Mamba a kwamitin dawo da kadarorin Gwamnati na babban kwamitin karbar mulkin na NNPP, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan yayin wani taron karfafa samar da bayanai a bincike ta hanyar aikin jarida domin yaki da cin hanci da rashawa ta amfani da harsunan Najeriya yau Asabar a Kano.
Cibiyar WADATA da WAMAC da tallafin gidauniyar MacArthur ne suka shirya taron.
“Daftarin bayanai a hukumance da aka samu ya nuna yadda aka karkatar da kudaden kananan hukumomi Biliyan 10 daga asusun gwamnati zuwa na daidaikun mutane, wannan daban ne da irin badakaloli da binciken mu ya gano”, inji Muhuyi.
Haka kuma ya ce irin ayyukan cin hanci da rashawa dake cikin gwamnatin mai barin gado shi kansa bai san su ba sai da ya shiga kwamitin karbar mulkin.