Home » Muyi Taka Tsantsan Wajen Cire Kuɗi a ATM Machine Domin Akwai Ƴan Damfara Jibge A Wurin

Muyi Taka Tsantsan Wajen Cire Kuɗi a ATM Machine Domin Akwai Ƴan Damfara Jibge A Wurin

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 2 minutes read

Daga Adamu Aliyu Tsiga

Jiya naje banki domin yin amfani da ATM na cire kuɗin da zanyi amfani dasu a wannan lokacin. Ko da na isa can sai na iske dogon layi. Sai ga wata budurwa ta zo ta same ni ta tambaye ni nawa nake son cirewa? Ya kamata ta cire 3k amma sai tayi kuskure ta danna 30k. Inji ta.

Yanzu za ta bani tsabar kuɗi har 20k, sai na tura mata a na ta account ɗin.

Abin da ya bani mamaki shi ne kamar minti5 ina tsaye akan layi kuma ban gan wannan Matar a kusa da wannan ATM ɗin ba, domin ba ta kan layi, ba ga kuma ga lokacin da ta cire kuɗi ba.

Sai na tambayi kai na shin da wanne ATM tayi amfani wajen cire kuɗin 30k ?

Sai na ce mata zan jira har layi na yazo, na kuma ce ta kauce da ganan ko na tozarta ta, sai na tambayi mutumin da ke gabana, shin ka ga matar nan a kusa da ATM lokacin da ta ke cire kuɗi ? Ina so in nuna masa ita amma matar ta ɓace, ban sa ke ganinta ba.

Na gaya wa mutumin abin da ta ce, sai ya yi dariya, ya ce ai wannan ba sabon abu bane. Suna zuwa ne da takardun Naira na bogi suna masu cewa sun yi kuskure sun cire kuɗin da bai dace ba.

Lokacin da ku kuma kuke gaggawa domin barin dogon layin da kuka tarar, kuna tura musu kuɗin ku kuma suna ba ku kuɗi. Ka fita da murna kana tunanin ka tsira daga dogon layi, sai ka je inda za ka sayi abun da kake so da Kuɗin sannan za ka gane an baka kuɗi na bogi.

Ƴan uwa mu yi taka tsantsan a wajen musamman wajen fitar da sabbin takardun Naira a halin yanzu mazambata suna nan cike da duk inda ake dabdala musamman inda ake hada-hadar kuɗi.

Allah ya tsare mu daga faɗawa hannun waɗannan mazambata. Allahumma Ameen…

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More