Home » Sakamakon fashewar wani a abu a jihar Rivers mutane da dama sun mutu

Sakamakon fashewar wani a abu a jihar Rivers mutane da dama sun mutu

by
0 comment 1 minutes read

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Fashewar wani abu ta afku da sanyin safiyar yau Juma’a a Rumuekpe da ke karamar hukumar Emeoha ta jihar Rivers, inda mutane da dama, da su ka hada da mata da yara da kuma motoci su ka kone kurmus.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare a wani wurin da ake hako danyen mai.

Da ya ke hira da manema labarai, Jami’ar hulda da jama’a na jihar Rivers, DSP Grace Iringe-Koko da ta tabbatar da faruwar lamarin a Fatakwal, ta ce amma har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

“Na kira DPO ya ce zai zagaya da tawagarsa na sintiri ya dawo wuri na. Ku jira kawai in samu cikakkun bayanai,” inji ta.

NAN ta tattaro cewa fashewar ta afku ne a yayin da wata motar bas dauke da danyen mai ta yi bindiga, yayin da ta ke barin wurin zuwa wata matatar mai ta haramtacciyar hanya a yankin.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More