Home » Shugabancin Majalisa: Su Doguwa Sun Janye Wa Abbas Tajuddeen

Shugabancin Majalisa: Su Doguwa Sun Janye Wa Abbas Tajuddeen

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 1 minutes read

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da takwarorinsa shida masu neman kujerar shugaban Majalisar sun janye wa janye wa Honorabul Tajuddeen Abbas.

Doguwa da sauran ‘yan takarar APC sun mara wa Abbas Tajuddeen wanda jam’iyyar ta tsayar domin jagorantar zauren majalisar na 10.

Sauran mutum biyu suka janye domin ba wa Abbas Tajuddeen damar jagorantar zauren majalisar na 10 su ne Abdulraheem Olawuyi da Abubakar Makki Yelleman.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai mai ci, Ahmed Idris Wase da Mukhtar Aliyu Betara da Miriam Onuoha da Yusuf Adamu Gagdi, su ma sun janye takararsu.

Doguwa da takwarorin nasa sun janye ne a cikin Laraba a wani zama da suka yi, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Femi Gbajabiamila da kuma dan takarar da jam’iyyar na kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio suka halarta.

A baya Doguwa da sauran mutum shidan sun yi watsi da zaben Abbas Tajuddeen da APC ta yi, suka kafa kungiyar G7 da nufin ganin daya daga cikinsu ya zama shugaban majalisar da za a zaba a watan Yuni.

Amma da yake jawabi a madadin sauran masu janyewar biyu, Doguwa ya ce, sun janye ne domin mutunta zabin jam’iyyar da kuma goyon bayan dan takarar shugabancin majalisar.

Ya ce sun kuma yi na’am da zabin uwar jam’iyyar tare da mara wa Abbas baya.

A masa jawabin, Sanata Femi Gbajabiamila duk da cewa dan jam’iyyar na iya samun sabanin ra’ayi da jam’iyyarsa, amma a baya jam’iyya ta yi irin wannan sasanci kuma ta ga amfaninsa.

Ya ce zabin da jam’iyyar ta yi, ta yi shi ne bisa la’akari da abubuwa da dama.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More