Home » ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tsohon Gwamnan Imo Hari, Sun Kashe ‘Yansanda 4

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tsohon Gwamnan Imo Hari, Sun Kashe ‘Yansanda 4

Mummunan lamarin ya faru ne a Oriagu da ke karamar hukumar Ehime Mbano, a daren ranar Litinin, inda aka yi wa ayarin motocin Ohakim kwanton bauna.

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 1 minutes read

Akalla mutum hudu aka kashe daga cikin ‘yan sandan tsohon gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim a ranar Litinin lokacin da ‘yan bindiga suka suka yi wa motarsa ​​kwanton bauna.

Mummunan lamarin ya faru ne a Oriagu da ke karamar hukumar Ehime Mbano, a daren ranar Litinin, inda aka yi wa ayarin motocin Ohakim kwanton bauna.

Ohakim, wanda ya tsira, an kai wa motar bayansa harin, inda aka kashe jami’an ‘yan sanda hudu da ke cikin ayarinsa.

Yana dawowa ne bayan ziyarar da ya kai tare da ‘ya’yansa guda biyu, kamar yadda majiyarmu ta samu.

A cewar wata majiya ta kusa da tsohon gwamnan, saurin da direban ya yi, ya bai wa tsohon gwamnan damar tserewa.

Majiyar ta yi ikirarin cewa tsohon gwamnan aka shirya kai wa harin, amma direbansa ya yi kokari wajen kubutar da su.

Sakamakon gaza cimma hakarsu, hakan ya sa maharan suka kone motar da ke biye masa baya.

Leadership Hausa ta samu labarin cewa wasu jami’an tsaro sun yi masa rakiya zuwa gidansa daga Owerri, babban birnin jihar.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More