Home » Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Kanal Din Soja Da ‘Ya’yansa 2 A Zamfara

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Kanal Din Soja Da ‘Ya’yansa 2 A Zamfara

by Maryam Sulaiman Muhammad
0 comment 1 minutes read

Wasu ‘Yan bindigan da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon-gaba da tsohon jami’in soji kuma jigo a jam’iyyar APC, Rabi’u Garba Yandoto da ‘Ya’yansa biyu da wasu mutum biyu akan hanyar Gusau zuwa Tsafe da ke jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin, Mohammed Hassan, ya shaida mana cewar Kanal Yandoto (Mai ritaya) yana kan hanyarsa ta zuwa garinsu tare da iyalansa a daren ranar Lahadi lamarin ya faru da shi biyo bayan farmakin da ‘yan bindigan suka kai musu suka kuma da wuce cikin daji da su.

Hassan ya ce, “Yan bindigar sun farmaki tsohon Kanal din sojan a daren ranar Lahadi kuma sun yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa biyu da wasu karin mutum biyu.

“Mun jiyo karar harbe-harbe kawai muka fara gudu domin neman tsira amma daga baya mun fahimci cewa masu garkuwar sun nufi kan Kanal Yandoto.”

Yandoto daya ne cikin Jagororin wata kungiyar APC da ke Zamfara mai suna ‘Wake Da Shinkafa’, sanannen mai adawa ne da Sanata Kabiru Garba Marafa.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Jami’in watsa labarai na hukumar ‘yansandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya citura zuwa lokacin da ya aiko da wannan labarin.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More