Rundunar yan sandan jahar kano ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Salisu , bisa tuhumar ta da soka wa karamar yarinya wuka a cikin ta.
A ranar Alhamis rundunar yan sandan jahar kano, ta gurfanar da matar,a gaban kotun Majistiri mai namba 39 dake zaman ta a unguwar gyadi-gyadi a kano, bayan kammala gudanar da binciken kan zargin da ake yi mata.
Ana tuhumar Fatima Salisu da aikata laifin yunkurin kisan kai.
Lauyar gwamnatin jahar Kano, kuma mai gabatar da kara Barista Khadija Aliyu Umar ta shaida wa kotun cewa sabuwar tuhuma ce a gaban kotun dan haka ta roki kotun ta bayar da dama a karanto kunshin tuhumar ga wadda ake zargin.
Mai shari’a Mustapha Hassan ya amince da rokon da lauyar gwamnatin jahar Kano ta yi, Inda ya sanya jami’in kotun Adamu Salisu Tarauni ya fassara mata da harshen Hausa.
Byan karanta mata tuhumar an tsaya Cik, babu batun haka ne ko kuma ba haka ba ne, Sakamakon rashin hurumin kotun ya sanya mai gabatar da karar ta bukaci a basu wata rana dan karbar shawarwarin lauyoyi.
Kotun ta amince kuma ta sanya kwanaki 21 dan karbar shawararin lauyoyin .
Manema Labarai sun ruwaito cewa, ana zargin Fatima Salisu da daukar yar makociyarta mai suna Sharifa Usman inda ta tafi da ita Unguwar Mariri a yankin karamar hukumar Kumbotso dake jahar Kano, tare da soka mata wuka a fatar cikin ta da kuma wasu sassan jikin ta.
Hakan ne ya sa aka kwantar da yarinyar a Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda ta ke samun sauki daga raunin da ta samu.
Tunda fari Fatima ta zargi mahaifin yarinyar da bawa mijinta shawarar karo aure, amma hakan bai yi mata dadi ba har ta dauki yarinyar ta kaita wani Kango ta soka mata wuka.
Sai dai abaya mijin ta ya musanta ikirarin nata, na cewa ana bashi shawarar karo aure kamar yadda manema labarai suka  ruwaito