A yayin da ake daf da fadar sakamakon zaben Gwamnan jihar Kano na karamar hukumar Dala, dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ne a kan gaba da tazarar kuri’u 102, 983.
Sai dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna ke biye masa da yawan kuri’u.
Tuni dai magoya bayan jam’iyyar NNPP suka fara murna a daidai lokacin da ake shirin fadar sakamakon karshe na zaben.