Home » Zaɓen Gwamna: Kwankwaso Ko Ganduje Waye Zai Karɓe Kano ?

Zaɓen Gwamna: Kwankwaso Ko Ganduje Waye Zai Karɓe Kano ?

by Salisu Hamisu Ali
0 comment 1 minutes read

Zaben Gwamnan jihar Kano da za a gudanar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris zai kasance fafatawa ne wajen iko da jihar Kano a fannin siyasa tsakanin Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2019 jam’iyyar APC ta lashe zaben da masu sanya idanu suka bayyana a wanda aka tafka kuskure da magudi wanda ya baiwa Abdullahi Umar Ganduje nasara.

Kwankwaso dai na da alaka sa Ganduje wanda ya kasance mataimakinsa tun 1999 zuwa 2016 lokacin da suka fara samun sabani.

A yayin da Gwamna Ganduje ke kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu, tambayar shi ne ko Nasiru Gawuna wanda ke samun goyan bayan Gwamnan zai iya yin nasara kan tawagar Kwankwasiyya dake da Abba Gida Gida a matsayin dan takarar ta.

Bayanai dai sun nuna cewa nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu a zaben ‘yan majalisun tarayya da na shugaban kasa a makwanni uku da suka gabata ya kara karfafa gwiwar magoya bayan ta.

A ganin magoya bayan Kwankwasiyya zaben na Gwamna zai zame musu masauki wajen samun nasara ganin yadda suka lashe kujerun ‘yan majalisu 17 da Sanatoci a jihar.

Sai dai a bangaren APC, tana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki ciki da wajen jihar Kano don ganin ta samu nasara a zaben.

A makon da ya gabata ne Gwamna Ganduje ya ziyarci tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau inda hakan baya rasa nasa da zaben Gwamnan da za a gudanar.

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More