Daga Rabilu Abubakar, Gombe
A lokacin da zaben gwamna da na yan majalisar Dokokin jiha ya rage kwanaki uku a gudanar da shi jam’iyyun siyasa 5 a jihar Gombe sun hade waje guda sun marawa takarar
Burgediya Janar Nuhu Millier Mai Ritaya na jam’iyyar AA Action Alliance
Shugaban jam’iyyar APGA na jihar Gombe Muhammad Mahdi Doho, ne ya bayyanawa manema labarai, dalilan su na hadewa dan marawa Burgediya Janar din baya.
Mahdi Doho, yace jam’iyyun da magoya bayan su sune suka yanke shawarin marawa dan takarar na AA baya dan ganin ya kada jam’iyyar APC mai mulki a zaben dake tafe na ranar asabar.
A cewar sa Millier gogaggen dan siyasa ne mai karamci wanda idan aka zabe shi zai ciyar da jihar Gombe gaba ya kuma samar da ribar mulkin democradiyya.
Mahdi, ya kara da cewa kafin daukar wannan matsaya sanda suka tattauna suka kuma nemi shawarin masu ruwa da tsaki sannan suka yanke wannan matsayar.
Shugaban jam’iyyar AA na jihar yace wannan hadaka za ta kara bai wa jam’iyyar AA damar lashe zaben.
Auwal, yace bayan sunyi wannan hadaka ta marawa Janar din baya yana mai kira ga al’ummar jihar da su fito su zabi dan takarar nasu domin cancanta.
Shi ma a nasa bangare Burgediya Janar Nuhu Millier, ya yabawa jam’iyyun 5 bisa wannan karamci da mara masa baya da suka yi wanda a cewar sa hakan na nuna cewa ya cancanci ya zama gwamnan jihar Gombe.
Janar Millier, ya hori magoya bayan sa da su kara nemo masa jama’a kan wannan takara tasa, sai ya roki matasa da su rungumi zaman lafiya su kuma tsaya tsayin daka dan ganin an jefa kuri’a kuma an zabe shi.
Jam’iyhun biyar da suka marawa Janar din baya sun hada African Action Congress (AAC) Allience Peoples Movement (APM) da Action Peoples Party (APP) da All Progressives Grand Alliance (APGA) sai kuma Accord Party (AP).
Â
Â
Â