Home » Zaben Radda: Jinjina ta musamman daga Adamu S. Ladan

Zaben Radda: Jinjina ta musamman daga Adamu S. Ladan

by admin
0 comment 9 minutes read

Daga: Adamu S. Ladan

Asabar ta gabata sha takwas ga watan Maris, 2023 ‘yan Najeriya sun sake kafa tarihi.

Tarihin da Ya kunyata wadanda ba sa wa kasar fatan alkhairi. Wadanda su ka hakaito cewa kasar za ta shiga rudami lokacin gudanar da zaben gwamnono da ‘yan majalisun jihohi bayan sun kasa cimma burin su a zaben da ya gabata.

Zaben na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da aka aje za a gudanar da shi sati daya kafin wannan lokaci, an dage shi zuwa karshen satin da ya gabata saboda uzurin da hukumar zabe ta bayar na cika ka’idar doka.

Wannan kuwa ya zama tilas don kada a ba wa wadanda ke hasashen rashin nasara a zaben kafar kawo cikas ta amfani shariah su dagula Lissafi.

Zaben dai an gudanar da shi cikin lumana kamar yadda hukumar zabe ta shirya a jihohi 31 daga cikin 36 dake fadin kasar nan.

Mutanen Najeriya sun ba makiyan kasar kunya inda su ka yi fitowar farin dango don sauke nauyin su na ‘yan kasa. Inda su ka zaba kuma aka ba su abin da su ke so.

Kamar yadda su ka yi a zaben da ya gabata makonni uku da su ka wuce su jefa kuri’un su sun bi doka sun yi abinda ya dace.

Duk da haka a daidaikun wurare wa su bata gari wadanda ba su da ta ido da iyayen gidansu su ka dora su bisa mumunar tarbiya sun bijiro da bakar al’adar nan da tuni an manta da ita ta yunkurin satar akwati, ko amfani da makamai don razana ma su kada kuri’a da kuma wadan su hanyoyin karkatar da hankalin ma su zabe daga zabin cancanta. Sai dai jami’an tsaro da sauran al’umma sun yi rawar gani wajen dakile su da tabbatar da cewa ma su wadan can bakaken aniyoyi ba su yi nasara ba.

A jihar Katsina, ma su jifa kuri’a sun ajiye bambamce bambancen jam’iyya su ka zabi cancanta. Inda su ka zabi Dr. Dikko Umar Radda da mataimakinsa Hon. Faruk Lawal Jobe bisa rinjayen kuri’u 859,892, ninkin mai biye ma sa na jam’iyyar PDP, sanata Yakubu Lado Danmarke Wanda ya samu kuri’u 486,620.

A nan dole a gode wa masu zabe a jihar Katsina saboda nuna kishi da wayewa a lokacin zaben. Inda su ka sa makomar jihar a gaba fiye da biyan bukatun daidaikun su.

Jinjina ta musamman ga jama’a da ke yankunan da ke fama da farmakin ta’addanci saboda bijire wa makircin makiyan al’umma, ma su zubda jinin su da tagayyara su don goga kashin kaji ga jam’iyyar APC saboda kawai su samu damar da za su mulke su.

Wadannan yankunan sun nuna hakuri da jajircewa matuka gaya inda su ka bijire wa duk wata tunzurawa don kawar da su daga mikakkiya hanayar da su ka taho ta zabar APC.

Bugu da kari yabo na musamman ga magoya bayan manyan jam’iyyun adawa na PDP da NNPP da PRP da su ka bar tafiyar su ka zabi Dr. Radda. Hausawa dai kan ce; ko da na ka, ka so nagari.

Haka ma wajibi ne a yaba ma kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar APC a jihar Katsina karkashin shugabancin jarumi mai hazaka, Jarman Kankia, Arc. Ahmad Musa Dangiwa wanda ya nuna juriya da hakuri da jajircewa da basira wajen gudanar jagorancin sa.

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna, Rt.Hon Aminu Bello Masari wadda ta samar da kyakkyawan yanayin da aka gudanar da zaben cikin cikkaken tsaro ba tare la’akari da kowane irin bambanci ba ita ma ta ciri tuta kwarai.

Wannan kuma shi ne ginshikin kammala zaben cikin lumana ba tare da wata hatsaniya da ta yi sanadiyar hasarar rai ko dukiya a kaf fadin jihar ba.

Kungiyoyin sa kai da na sa ido na cikin gida da na waje ma sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da aka samu a zaben. Kungiyoyin sa kai musamman ta fannoni tsaro sun bada gagaruma gudumuwa ta cike gibin da ke akwai inda jami’an tsaro ba su isa ba. Na tabbatar da wannan a karamar hukuma ta, ta Dandume wadda ke fama da matsanancin matsalar tsaro.

Za a yaba wa kungiyoyin sa ido saboda sabanin wa su lokuta ko wurare inda irin wadannan kungiyoyin ke shirya rahotonni karya don su kawo tunzuri ko rudani ko su bakanta zaben. A wannan karon kuma a jihar Katsina ba a samu hakan ba a fili.

Jami’an tsaro ma sun nuna kwarewa yayin gudanar da aikin su. Sun sa jarunta da bin ka’idodin aiki na ba sani ba sabo wajen dakile duk wata barazana da ta nemi ta dagula Lissafin gudanar da zaben.

Yanzu dai a fili ya ke mutanen jihar Katsina sun zabi gwamna da aka yi wa jam’iyyar sa ruwan kuri’u kusa da dubu dari tara 900, 000 tare da rinjayen ‘yan majalisu dari bisa dari.

Wannan na nuni da Ya cewa ma su jefa kuri’a sun tattara soyayyar da su ka nuna wa manyan ‘yan takarar shugaban kasa guda biyu, watau Tinubu da Atiku a jihar Katsina sun mika wa Dr. Radda.

Lallai wannan babban tagomashi ne a siyasa. Sai dai hakan na tattare da babban kalubale ga zabbaben gwamna mai jiran gado, Dr. Radda. Kalubale na kyakkyawan fatan da mutane su ke da shi a kan sa na zai iya fitar mu su kitse daga wuta.

Duk da cewa Dr. Radda tun yakin neman zaben sa ya yi ma mutanen jihar Katsina alkawarin gudanar da mulki bisa doran adalci, ya sake jaddada haka bayan hukumar zabe ta ayyana shi a matsayin zabebben gwamna.

Ba ma shakku bisa cancanta Dr. Radda wajen fuskanta wannan kalubale.

Kamar yadda mu ka shaida ma jama’a kafin zaben ranar Asabar. Dan shekaru 54, Dr. Radda gogaggen dan siyasa ne, kwarere kan harkar zuba jari, tsohon malamin makaranta, da aikin banki kuma goggen masanin tafiyar da mulki.

Yayin yakin neman zabe ya nuna kan sa a matsayin jagora, lafiyayye, tsayayye, mai dogaro da kansa, mai ilmi kuma kwarare a fannoni na rayuwar aikin gwamnati da kuma mai zaman kan sa.

Ya kuma nuna cewa shi ba yankan rake, ko dan bani na iya ba ne.

Baya ga fitowa daga babban gida, Dr. Radda ya sa mu kyakkyawar sheda cewa mutum ne mai tarbiya da halaye nagari da iya mu’amala da hangen nesa.

Ya na kuma da tausayin na kasa da marasa galihu. Ya kan nuna matukar damuwarsa kan al’amarin al’umma.

Duk da wadannan halaye, Dr. Radda ba mutum da aka yi wa hawan kawara ba ne musamman kan abun da ya shafi gudanar da mulki da jama’a. Ya iya tawaye akan duk wata manufa da ya ke ganin ba za ta haifar ma jama’a da mai ido ba.

Wadanda su ka yi aiki da shi kud-da-kud sun ba da shaida cewa ya na da tsinkaye da hangen nesa wajen daukar shawara da yanke hukumci. Ya na da kuma gogewa da tsantseni wajen tusarrafi da dukiya al’umma.

Dr. Radda ya nuna cewa jagora ne nagari.
Daga tanade tanaden da ya yi cikin kundin da ya gabatar wa jama’a zuwa rangadin da ya gudanar da kalaman sa ya nuna cewa ya shirya tsab don jagorancin jihar Katsina. Shiri irin na fitar da kitse daga wuta.

Kundin da ya gabatar ya kunshi manufofi da kudure kuduren sa game da jihar Katsina da kuma hanyoyin da za a cimma su. Wadannan kudurori ba shaka idan an aiwatar da su ba kwai za su tabbatar da dorewar cigaban da aka samu karkashin jam’iyyar APC ba ne har ma za su samar da sabuwar jihar Katsina.

Manya daga cikin tanade-tanaden su ne; harka tsaro, da fannoni ilmi, da harkar lafiya, da aikin gona, da samar da aikin yi, da zuba jari da masana’antu, da cigaban matsa, da inganta aikin gwamnati, da inganta birane da kuma raya karkara.

Don samar da cikaken tsarin aiwatar da wadannan kudare kudare yanzu haka an nada wa su kwamitoci da su ka kunshi kwararu daga fannoni na rayuwa dabam dabam don zayyana hanyoyin da za a cimma wannan buri. Mu na sa ran ba da dadewa ba za a kaddamar da wadannan kwamitoci don fara aikin su.

Hausawa sun ce; gani ya kori ji. Tuni dai Dr. Radda ya gudanar da rangadin kananan Hukumomin jihar Katsina guda talatin da hudu (34). A wannan tsarin an gudanar da rangadin da kusan shekaru arba’in ba a yi irin sa ba. Inda aka shiga kowace mabaza ta kansila watau ward guda 361.

A lokacin rangadin, Dr. Radda da tawagar sa sun gane wa idanuwan su halin da kowane lungu da sako na jihar Katsina ke ciki.

Sun kwana cikin garuruwan, sun ci abinci kuma sun sha irin ruwa da jama’a kowace karkara ke ci da sha. Sun kuma ga cigaba da akasin haka na wadannan yankunan.

Saboda haka ana sa ran gwamnatin da za a kaddamar ba za ta dauki dogon lokaci ba wajen tunkarar abin da ke gaban ta.

Fata ita ce, Allah Ya kama hannun sa Ya yi ma shi jagora wajen zabo wazirai na gari da za su tallafa ma sa aiwatar da wannan gagarimin aiki.

Ya na da kyau kuma mu yi amfani da ibada da mu ke a wannan wata mai alfarma don yi wa Allah godiya da Ya sa aka yi zaben lafiya sannan Ya zaba mana ma fi alkhair. Haka kuma mu nema ma sabon gwamna jagorancin Ubangiji da kariya wajen gudanar da mulkin jihar Katsina.

Yayin da mu ke wa sabon zabbaben gwamna fatan alkhair ya na da kyau kuma jama’a su yi amfani da wannan lokaci da ake shirye shiryen mika mulki wajen bayar da nagartattun shawarwari da za su taimaka don ciyar da jihar Katsina gaba.

Ga wadanda Allah bai ba su nasara ba, su ma mun jinjina ma su da su ka shiga zaben. Shiga su ta haska kuma ta ba jama’a dama su ka zabi ma fi nagarta. Ta kuma zaburar da jam’iyyar mu ta hanyar abinda a ke cewa in kana da kyau ka kara da wanka.

Saboda haka ya na da kyau a wannan gabar a bada shawara ga wadanda ba su sami nasara ba da su rungumi kaddara kamar yadda su ka sha fada lokacin yakin neman zaben su. Maimakon daukan matakan da ba za su haifar da da mai ido ba. Ya kamata su bada hadin kai ga wanda Allah Ya zaba ta hanyar yin adawa mai ma’ana da a koda yaushe za ta saita gwamnatin da za a kafa bisa tafarki ma daidaici.

Adamu S. Ladan
Dan kwamitin wayar da kai, na kwamitin yakin zaben jam’iyyar
APC na jihar
Katsina

You may also like

Leave a Comment

About Us

We are a media platform published by Prime Time Newspapers Limited, based in Kano. its committed to passionate, insightful and objective coverage on democracy, governance, business, security and humanitarian values.

Feature Posts

Newsletter

Subscribe my Newsletter for new blog posts, tips & new photos. Let's stay updated!

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More