Shugaban majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiama ya ce a shirye yake ya baiwa babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya umarnin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele domin sanya shi ya gurfana gaban majalisar.
Gbajabiamila ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da yake mayar da martani kan rahotan da shugaban kwamitin riko na majalisar da ta kafa dan shiga tsakanin Bankuna da babban bankin kasar karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Doguwa.
Doguwa ya shaidawa majalisar cewa Bankin CBN da Emifiele basu amsa gayyatar kwamitinsa ba a ranar Laraba.
Sai dai shugaban majalisar ya ce zai yi amfani da damar kundin tsarin Mulki ya bashi wajen baiwa ‘yan sanda umarnin kama Gwamnan Bankin domin tilasta masa ya gurfana gaban majalisar.