Daga Mustapha Salisu
Kungiyar Hadin Gwiwar Kasa ta Mutanen da ke da Bukatu na Musamman (JONAPWD), reshen Jihar Kano, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta daukar matakai domin inganta damar samun kulawar lafiya ga masu bukata ta musamman a jihar.
Shugaban kungiyar na Kano, Injiniya Musa Muhammad Shaga, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani tattaunawa da wakilin PRIME TIME NEWS, Mustapha Salisu.
Injiniya Shaga ya bayyana cewa mafi yawan cibiyoyin lafiya a jihar – daga matakin farko har zuwa na gaba – ba su da kayan aiki da kayayyakin da suka dace da bukatun PWDs kamar wheelchairs, gadon asibiti na musamman, da wuraren shiga da suka dace.
“Ko wurin da ake bayar da kati a asibiti ba ya dace da mu. Misali, wurin bada katin yayi sosai wanda ya fi karfin me bukata to musamman ko wanda ke kan keke” in ji shi.

Ya kara da cewa, ma’aikatan lafiya da dama ba su da horo kan yadda za su mu’amala da masu bukata ta musamman. “Yadda suke magana da mu da kuma kallon da ake yi mana yana sanya mutum ya fi so ya koma gida da ciwo maimakon ya zauna a asibiti,” in ji shi.
Injiniya Shaga ya bayyana cewa akwai manufofi da dokoki da ke kare hakkin masu bukata ta musamman a fannoni daban-daban, amma rashin hukuma mai sa ido da tabbatar da wadannan manufofi na hana aiwatar da su yadda ya kamata.
“Wannan ne dalilin da ya sa muke kira da a kafa Hukumar Kula da Masu Bukata Ta Musamman ta Jihar Kano domin tabbatar da wadannan hakkoki,” ya jaddada.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar, Aminu Ahmad Tudunwada, ya bukaci gwamnati da ta dawo da tsohon tsarin inshorar lafiya da ke rufe ma’aikatan gwamnati da ke da bukata ta musamman, tare da iyalansu – wato mata da yara hudu.
“Abin takaici, tun da aka cire wannan tsari, da zarar yaro ya kai shekara 18 ko 20, za a cire shi daga inshorar. Muna rokon a dawo da tsarin har sai ma’aikacin ya yi ritaya ko kuma ya rasu,” in ji shi.
Wakilin PRIME TIME NEWS, Mustapha Salisu, ya ruwaito cewa JONAPWD na da rassa a dukkan jihohin Najeriya 36 har da Babban Birnin Tarayya (FCT). Kungiyar na tallafawa mambobinta a fannoni daban-daban. Daya daga cikin manyan nasarorin da ta samu a Kano shi ne kudirin ilimi da aka yi karkashin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya baiwa ‘ya’yan PWDs damar samun ilimi kyauta daga firamare har jami’a a makarantun gwamnati. Da dama daga cikinsu sun kammala karatu tare da samun ayyuka a sassa daban-daban na kasar.
Haka kuma, kungiyar na horar da mambobinta a sana’o’in hannu domin dogaro da kai, ciki har da kera kekunan guragu da sauran kayan bukatu a cikin gida maimakon dogaro da kaya daga waje. Wasu daga cikinsu na kera kayan wasa na makarantu kamar ‘merry-go-round’ da makamantansu.
Wasu daga cikin kere-keren su sun hada da: